TAMBAYA: Shehi barka da zuwa wannan fili mai albarka.
DAKTA YUSUF ALI : Assalamu alaikum warahmatullah wa barkatahu. Allahumma salli ala Muhammad wa alihi, wasahbihi wasallim.
TAMBAYA: Daga Bashir Magashi. Malam ina tambaya ne a kan ilimin badini. Ana zuwa ne makaranta a koya a cikin littafi, ko ya yake?
DAKTA YUSUF ALI : Shi ilimin badini wani ilimi ne da ake raya zuciya da shi, ake kuma tsarkake zuciya da dukkan wani abu da ya zamanto najasa ne. Kamar yadda siffofin kamala suke, to haka nan ma yawan siffofin nakasa suke. Kamar wani son girma, son duniya, su hassada, su kullata mutane da gaba. Da abubuwa irin su riya, sabanin nakasa ta zahiri wanda mutum zai zo ya aikata. Kamar a ce zina ko a ce sata. Ilimin badini ana maganin cututtuka ne na cikin zuciya da shi. Matukar karshensa dai shi ne a samu gushewar wadannan nakasoshi na cikin zuciya da shi. Hanyoyin da ake bi a takaice sune hayar da za a bi a tsarkake zuciya, wanda mutum har zai kasance bayan ya tsarkaka, zuciyarsa ta dace da saduwa da halaran Ubangiji Allah (SWA).
In mutum ya ga cewa abubuwan ya kasa ganewa, to Allah (SWT) a ayar karshe cikin suratul Ankabut yana cewa "Wadanda suka yi kokari za mu shiryar da su zuwa tafarkanmu." Ka ga kenan ba tafarki daya aka ce ba. Akwai wata aya a cikin suratul An'ami, inda Allah ya ce, "Hanyar nan guda daya ce, ku bi ta. Kada ku bi hanyoyi sai su batar da ku." Akwai Islam. Akwai Iman. Akwai Ihisan. Uku kenan ko? To wadansu sukan raba wadannan. Iman da Ihsan su ke kamar ana maganar ilimin badini ne. Amma ihsan ya fi zama ilmin badini sosai, don saboda za ka bauta wa Allah ne kamar kana ganin sa. In ba ka. Ganinsa shi fa yana ganin ka. Ko kuma a raba shi a ce akwai shari'a, akwai hakika, akwai darika. Wannan Malaman Musulunci sune suka raba wannan, musamman idan ka duba manya- manyan littattafai da suka fassara hadisin nan na Sayyadina Umar, ko kuma hadisin Mala'ika Jibrilu da ya zo wurin Manzon Allah (SAW) yana tambayar sa. Da farko ya tambaye shi menene Musulunci? Ya gaya masa. Ya sake tambayar sa menene imani? Ya gaya masa. Menene ihsan? Ya gaya masa. To wannan shi ne aka rarraba haka. Wanda bai fahimci Musulunci a kan haka ba, to ya yi masa fahimtar da ba haka nan shi Manzo (S) ya fahimta ba.
Kuma Allah ya aiko ma Annabi Mala'ika ne, don saboda bayan da shi Mala'ika Jibrilu ya tashi ya tafi, sai Annabi (S) ya ce "Mala'ika Jibrilu ne ya zo ya sanar da ku addininku." Saboda Manzon Allah ko da ya sanar da su watakila ba zai zauna a zuciyarsu ba. Wannan ita ce hikimar da ta sa akan gayyato wadansu malamai su zo su yi wani jawabi. Kamar a ce a makaranta a kirawo wani Malami, bayan kuma a makarantar nan Malamai ne. Akwai wata manufa da ake so ta zauna a zuciyar dalibai. Kamar dai da malaman sune za su fada daliban ba za su rike sosai ba. To wannan shi ne. Sai Allah SWA ya aiko Mala'ika Jibrilu saboda wannan manufa. Ya gaya musu ga yadda rabe-raben addinin yake. Ilimin zahiri, akwai na fakaice. Akwai ilimin badini. Za kuma a iya saka littafi mana wajen koyar da shi. Akwai littafai da suka yi magana a kan irin wannan ilimin. Akwai irin su Al-kusheriyya, kamar irin su ihya'u ulumid dini, irin su Kutul Kulubi. Duk ga su nan dai ire-irensu. Ko kuma Futuhatul gaibi na Shehu Abdulkadir. Za a iya saka irin wadannan a karanta su. Amma kuma gwargwadon zurfin fahimtar mutum a ciki. Gwargwadon kokarinsa shi ma zai iya fahimtar wadansu abubuwa da kansa a ciki. Kuma kamar fassarar Kur'ani, an ce tana da fassara na zahiri da na badini. Zahiri kaman guda daya, amma badini za a iya fassara shi kamar sau bakwai. Wadansu sun ce ma har sau saba'in ma a aya daya za a iya samu na fassarar badini. Wannan shi ne amsar da za mu ba ka.
TAMBAYA: Akwai dangantaka ne tsakanin ilimin sufanci da na badini?
DAKTA YUSUF ALI : Ai da ma, tunda an ce ilimin sufanci an gina shi ne a kan tsarkake zuciya daga dukkan abubuwan da suke gurbata zuciya. Idan an ce zuciya ta lalace, dukkan jiki ma ya lalace. Haka Manzon Allah (S) ya ce, akwai wata gaba a cikin jikin mutum, idan ta gyaru duk jiki ya gyaru, idan ta baci duk jikin ya baci. Ita ce zuciya. Su Malaman sufaye abin da suka damu da shi shi ne suka dukufa wajen tsarkake wannan zuciya wadda Annabi (S) ya ce in ta gyaru, jiki ya gyaru. Shi ne ma ya sa Malamai masu bincike suka tabbatar cewa a wannan manufa Annabi (SAW) shi ne ma sufin farko, wanda dukkan ayyukansa ayyuka ne na tsarkake zuciya, ayyuka ne na gudun duniya, ayyuka ne na tawali'u. Kullum bai damu da tara abin duniya ba, bai kuma damu da a girmama shi ba da wadansu hidimomi, duk yana hanawa. Wannan shi ne abin da aka gina sufanci a kansa, gyaran zuciya.
TAMBAYA: Daga wata baiwar Allah ce. Malam matsalata ita ce idan na kwanta barci sai in ji ana min kara a cikin kaina. In na farka sai in ji kamar mutum ne a bayana. In zan juya sai in ji kamar an rirrike ni, ana yi mani kara a cikin kaina. Sama da shekara tara kenan ina fama da wannan matsala, shi ne nake so in ji ko Malam zai taimaka mani da wani taimako da zan rabu da wannan matsala?
DAKTA YUSUF ALI : Wadannan abubuwan da kika lissafa gaba daya hanyoyi ne irin na cutar Aljanu. Dama akwai wadanda a fadake ake gamuwa da su. Akwai kuma wadanda sai a barci. Abubuwa biyu daga cikin abin da kika fada sun isa a yanke hukuncin lallai cewa akwai sharrin mutanen boye a ciki. Hanyoyin da ake maganin mutanen boye shi ne ake bi. Rashin barcin nan ko ki ji ana miki kara ko ki ji motsi a bayanki duk sune. Babu abin da za a yi illa kawai magani kai tsaye da muke bayarwa. Lokacin kwanciya barci za ki yi addu'a. Safe da yamma za kuma ki rika zama da alwala, da kwanciya da alwala. Nisantar wadansu abubuwa, da yin sallah a kan lokaci, da nisantar kade-kade da kuma kokarin yin karatun Kur'ani da yawaita karanta kalmar shahada. Za kuma ki rika karanta fatiha da Amanarrasulu da ayatul Kursiyyu in za ki kwanta. Ki hada hannayenki ki karanta Kulhuwallahu da falaki da Nasi, ki shafe duk jikinki. In dai rashin barci ne, kina karanta wadannan insha Allahu za ki rika samun yin barci.
TAMBAYA: Ina sanar da Malam in ina karanta ayatul kursiyyu sai in ji ana mayar min.
DAKTA YUSUF ALI : Maganar dai duk daya ce kike yi. Na gaya miki da za ki fadi abubuwa na wane, maganar dai ita ce kawai ki jarraba wadannan abubuwa da aka fada miki, ki ci gaba da yin su ki gani. Insha Allahu bayan sati uku in ya kasance ba ki daina jin su ba, sai a baki wasu da za ki yi, insha Allahu kuma kin rabu da su.
TAMBAYA: Hajiya Safiya ce. Tambayata ita ce wani bawan Allah ne yana da mata guda uku, sai ya kasance ya samu matsala ta rashin lafiya. Ya kasance in bayan gida ya kama shi kafin ya je makewayi zai yi abin sa a wando, sai kuma matan nasa suka kaurace masa, shi ne abin ya shige musu duhu, shi ne suka ga ya kamata a yi tamabaya a kan me ye abin da ya kamata su yi?
DAKTA YUSUF ALI : Abin da ya kamata shi ne bai kamata a kaurace masa ba. Na tabbatar da su ne suka shiga cikin wannan halin ba zai kaurace musu ba. Ai Allah (SWT) ya shardanta aure ne don a samu kauna da tausayi ma juna da natsuwa da juna. Saboda haka ba daidai bane su kaurace masa. Kaurace masa yana dada masa kamarin abin. Idan suna tare da shi zasu iya gane abin da ke damun sa, ana iya zuwa asibiti. Idan an ga abin ba na asibiti bane ana iya neman magani wanda zai iya warkar da wannan cuta. Kin gane ko? Saboda haka ba a ce mace ta kaurace ma mijinta ba. Idan kuma ya name ta lallai ne idan ba wata shari'a ba ko tana wata al'ada lallai ne ta je masa ko da tana suya ne a tanderu ko da a kan rakumi ne. Saboda haka in ta ki ta sabi Allah. In kuma ta ga ba za ta iya zama ba, to ta kai kara a duba a gani in akwai cuta a raba su.
TAMBAYA: Tambayata ta biyu ita ce, Malam akwai lokacin da na taba yi maka waya a gidan rediyon Jigawa a kan wata lalura tawa, har ka ban shawarar cewa akwai wasu abubuwa da ya kamata a yi. Har na turo mijina ya zo ya karbi wasu takardu da ka bayar da wasu bayanai, kuma an bi hanyoyin, amma har yanzu Allah bai kawo karshen abin ba.
DAKTA YUSUF ALI : Ai duk abin da muke bayarwa, in dai da hannuna na bayar, aka zo aka karba a gidana, tsananin abin sati uku muke cewa. Wannan lallai ne insha Allahu za a samu waraka. In ko ba a samu ba, sai a dawo a sake yi mana bayani, ga shi na je sati uku, ko dai abin ya karu ne, ko ya ragu, ko har yanzu yana nan kamar da. Kowane daya akwai hanyoyin da za a bi, insha Allahu sai a gyara. Ina jin wannan maganar za ta kai shekara daya ko biyu ko? (A'a, ba zai kai shekara ba) To sai ki sake turo wa, sai a sake yi ma mijin naki bayani.
TAMBAYA: Tambayata ta karshe. Ina so Malam ya yi kira ga Magidanta masu shiga gidajensu ba tare da sallama ba. Kuma in sun shigo gida sai ka ga ransu a bace, amma a waje fuskarsu a sake, har suna wasa da dariya. Amma suna shigowa gida sai su hade fuska, kuma ba tare da matayen nasu sun musu wani laifi ba.
DAKTA YUSUF ALI: To dai in dai shigowa yake ransa a bace a durkune a kasa gane kansa, Manzon Allah (S) ya ce Allah (T) ya la'anci wanda zai kasance a gidansa kullum kunkume yake kamar wani zaki. Manzon Allah ya ce Allah dai ya la'anci irin wadannan mutane. Manzon Allah (S) yakan zamo kamar wani yaro a cikin gidansa wajen sakin fuska ga iyalinsa. Idan ka dubi Sayyadina Umar, duk irin tsananin nan nasa, amma a cikin gidansa matansa juya shi suke yi, sai dai idan wani abin ne ya tashi na maza sannan ne za a gane shi ma jarumi ne. Wannan shi ne sunnar Manzon Allah (SAW). Yadda kuma ake yin zama kenan. Babu wani fada a ciki, babu wani daure fuska, ai abokiya ce ta zaman duniya.
A kan maganar kin yin sallama. Sallama a gane kwankwasa kofa da gyaran murya duk wannan yana iya zama kamar wata sanarwa. Sanarwa ce in maigida zai shigo. Babu yadda za a yi sai Maigida ya yi gyaran murya. Haka za ka ga ya kirkiro tari ya ce ohol, na nuna alamar cewa ga shi nan shigowa. In kuma mutum tafiya ya yi ya sauka kamar da dare wajen karfe goma sha daya da minti biyar din nan, to addinin Musulunci ya hana shi ya je gidansa yanzu. Lallai ko ya kwana sai da safe ya je ya gan su, kuma kafin ya je ya aika cewa ya dawo. Yanzu lokaci ne da ba aminci, kuma ballantana akwai ayar Kur'ani da take cewa "Fasallimu ila ahlikum." Ku yi sallama ga iyalanku, "Tahiyatan minallah mubarakatan dayyiba." Gaisuwa ce daga Allah kai Maigida. Idan ka zo ka ce "Assalamu Alaikum warhamatulla." To ka isar da gaisuwar Allah zuwa ga iyalanka. Da akwai wani mutum a zamanin Manzon Allah (SAW) da ya kawo karan talauci, ya ce ya Rasulullahi ba ni da komai; duk hanyan da zan kama don in samu arziki babu. Sai Manzon Allah ya ce sallama ce ba ka yi. Abin da za ka yi idan za ka shiga gidanka ka yi sallama.
Idan ba kowa gidan ga irin sallamar da za ka yi. In akwai mutane ka ce "Assalamu alaikum warahmatullahi wa barakatuhu." Idan kuma ba kowa ka ce "Assalamu alaina wa'ala ibadallahi salihin. Assalamu alaikuma warahmatullah watahiyyatan minna wabarakatan minna." Sannan ya karanta Kulhuwallahu kafa uku. Mutumin nan daga farawa dinsa din nan sai arziki ya kwarara. Ba ma shi kadai ba, kai har ma makwabtansa. Saboda albarkar sallama da yake yi in zai shiga gidansa da kuma karanta kulhuwallahu din nan. Saboda haka wadanda ba sa sallama tamkar suna cutar kansu ne, don ko suna rage wa kansu arziki ne.
TAMBAYA: Daga Alh. Baba. Gafarta Malam ina tambaya ne a kan halwa. An ce mutum zai iya shiga ya kwana arba'in, to amma kuma zai zauna ne a gida shi kadai, to wajen maganar sallah fa ta jam'i, a nan ne kaina yake daurewa.
DAKTA YUSUF ALI : To wajen sallar jam'i. Lallai sallar jam'i tana da girma sosai. Har ma Manzon Allah (S) ya kawo muhimmancinsa sosai. Masu kaurace ma jama'a da kuma masu shiga cikinsu. Malamai sun yi maganganu a kai. Akwai abin da ake ce ma al-uzla. Malamai sun wallafi littafai sukutum kamar irin su Sulaimanu. Sun wallafa littafai a kan uzula din nan. Kuma har yanzu in ka dauko littafai manya-manya, misali irin su lhya'us sunna, irin dai littattafai da suka wallafa da suka hada komai da komai. Sun ware babi wanda yake zancen uzla-uzla, kamar kaurace ma jama'a kwata-kwata, mutum ya koma ga Allah. Wannan shi ne ya sa Imam Malik a karshen rayuwarsa gaba daya, ya daina zuwa sallar jam'i gaba daya.
Ya daina zuwa sallah, ya daina zuwa taron jama'a duk wanda ake yi, ya yi zamansa kawai. Kuma Annabi (S) lokacin da wani yake tambayar sa a kan fitina-fitina, shi kuma sahabi ne. Banda fitina babu abin da yake tambayar Annabi (SAW). Manzon Allah ya ce idan aka kai wannan lokaci ka zama lazimin zaman dakinka. Malamai sun raba irin wadannan hadisai. Sun raba cewa idan ya kasance mutumin nan ya zama in ya fita cikin jama'a, zai amfane su, akwai amfana da za a yi da shi, shi ya amfana da su, to ya shiga ya amfanar da jama'a din.
An ce Shehu Abdulkadir an gwada shi da wani Malami. Yake cewa na fi shi. Aka ce ah, to me ya sa ka fi shi? Saboda ni ina fitowa cikin jama'a ina amfanar da su. Shi ko sai ya yi zamansa a cikin gida.
Shi ko maganar halwa wani abu ne da ya shafi mutum shi kadai. Abin nan ba wai farilla bane, sai dai kawai abu ne na ja'izi. Mai yiwuwa zai kasance a lokacin da yake tafiya sallar jam'i din, sallar ta zame masa ba ta da wani amfani don saboda ba ya yin hururi, ko bai fahimci Allah a cikinta ba. Amma kila in ya ware kwana bakwai ko kwana arba'in ya zauna yana ba da sallar nan a kan lokacinta, kamar yadda ya kamata, amma kuma ya koma ga Allah ya fuskance shi da kyakkyawan niyya a kan cewa ya fahimtar da shi wani abu wanda zai kasance ya gane addinin nan. Bayan kwana arba'in din nan ya fito, ka ga kenan wannan za a ce wannan halwa da ya shiga ta amfane shi, kamar yadda mai Ishiriniya yake cewa "Bi gairi hira'in mufuradan mutuhannasu." Wato Manzon Allah (S) ya kaurace. Kullum idan watan azumi ya zo yakan kaurace a kogon hira, shi shi kadai yana ibada. To irin wannan ne. Wani kuma yakan shiga halwar nan saboda neman abinci ne kawai. Duniya ce ta riga ta toshe masa saboda haka ya samo wasu ayoyi ko wadansu sunayen Allah yake karantawa don Allah ya yi masa budi, amma aka ce sai ka nisanci hayaniyar jama'a don ka samu natsuwa. Yana ganin ba zai samu kwanciyar hankali ba a game da adddini sai ya samu dan abin da zai ci shi da iyalinsa. Saboda haka wannan wuridi da yake yi kuma ba ya samun damar halartar sallar jam'i, to nan ya zama yana da uzuri. Saboda dole ne ta sa shi kauracewa. Ka ga kenan akwai wanda zai nemi abinci, akwai kuma wanda zai nemi kusanci da Allah ta hanyar halwa. Amma wanda zai nemi abin da zai zo ya cuci mutane, ko ya nemi Aljanu su rinka yi masa hidima, a aiki wancan a kaso wancan, ko a raba auren wancan, to wannan haramun ne. Wanda yake yin wannan, in har ya yarda da hadisin Manzo (S). Ba ma shi ba, wanda ya je wurinsa, shi ma ya kafirta, in ya gaskata abin da yake yi. Saboda haka ya kamata mu rarraba abubuwan nan. Duk abin da aka ce Musuluncu ya zo da shi, Malamai sun yi magana a kansa, wasu suna yi, wasu ba sa yi, wannan gaba daya ba za ka ce ka rushe shi ba. Sai ka duba ka ga meye aka ce a ciki. Alal misali ka ga an ce a cikin darikar Tijjaniya babu zancen halwa, a yadda kake din nan za ka samu biyan bukata. An ce lokacin da Manzon Allah ya sanar da Shehu Tijjani darika cewa ya yi "da haka za ka samu biyan bukatunka, ba sai ka kaurace wa jama'a ba." Duk wadannan halwowin da ake yi a cikin darikar Tijjaniya daga baya ne aka shigo da su, amma aslin abin babu, kamar yadda Manzon Allah ya yi lamuni ga shi Shehu Tijjani.
TAMBAYA: Shi kuwa ilimin hisabi fa?
DAKTA YUSUF ALI: Ilimin hisabi, shi ma akwai wanda yake halas ko kuma wajibi. Kowane gidan Malami a nan Kano idan kana karatun littafi wala'alla kana karanta Risala ne ko Iziyya ko Muktasar ko Akarabul masaliki, ko Askari, duk sadda aka zo babi na fara'il, wato babin gado, to fa littafan sai a mayar da su wuri daya, Malami ya ajiye nasa kai ma ka ajiye naka. A jawo katako a shimfida kasa, to sannan kuma sai a fara koya wa dalibi hisabi. Sai ya sa tun daga daya har zuwa goma, ya sa duk hukunce-hukunce har ya zo inda zai buga ya ce baggadun, duk sai an san wannan. Akwai wanda yake neman rabi, wani sulusi, akwai mai neman sumuni, akwai mai cinyewa duka. Ka ga in bai iya lissafi ba ya zama Malami? Kuma in za a yi rabon gado sai ya nemo wani, to ka ga wannan akwai tawaya. Har yanzu kuma ai akwai aya wacce take cewa ba don komai Allah ya sako rana da wata da taurarin nan ba, don ku san kididdigan shekarau da hisabi ne. To ka ga irin wannan hisabi gwargwadon wanda zai ganar da kai yadda za ka tafiyar da harkokinka halas ne. Hisabi ya kamata a gane lissafi kenan.
Amma hisabi, wanda aka zurfafa har aka rika duba da shi, akwai wanda zai zamo haramun, wanda za a rika bugawa ana gano gaibi ko kuma a buga a ce mace mai ciki ce. A buga shi a raba da hudu, idan daya ya yi saura, a ce dan da ke cikin zai rayu din. Idan guda biyu ya yi saura za ta haifi namiji. In uku ne mace ce. In hudu ne bari ne. Kamar irin wannan da dai sauransu. To ka ga irin wadannan bai kamata a ce an halasta shi ba. Amma dai akwai a cikin littattafan Malamai, yana nan, irin su Abu Ma'asharar faki din nan, irin su Alfasilu fi ulul Ramli da sauran irinsu. Wadannan za a dauke su haramun ne. Amma ilimin hisabi, wanda za a gane harkokinka su tafi daidai yadda ake rabon gado, wannan irinsa sai a ce wajibi ne. Alal misali idan ka dubi ilimin kwamfutan nan, duk lissafi ne. Yanzu babu yadda za a yi a ce rayuwa ta zo cikin sauki sai da kwamfuta.
TAMBAYA: Yanzu abin da jama'a suka raja'a a kai shi ne su je a duba musu, ko an jefe su ko wani abu mai kama da irin wannan, shi kuma ya yake?
DAKTA YUSUF ALI: Wannan muka ce bai halasta ba. Ba ma wanda yake yi ba, wanda ya je gurin irin wadannan ma ya gaskta su, ya zama kafiri. In bai gaskata su ba, zuwa kawai ya yi, ba shi da sallar kwana 40. In ko zuwa ya yi domin ya gano illar abin, wannan shi ba komai a kansa. Saboda Manzon Allah (S) ya je wajen Ibn Sayyad, wanda boka ne ya kuma tabbatar boka ne. Saboda haka bai ce hakan da ya yi laifi ne ba. Saboda haka wani hadisi na Manzon Allah (S) yana cewa wanda duk ya je wurin boka ko dan duba ya gaskata shi da abin da yake fada, to hakika ya kafirta.
TAMBAYA: Malam wata mata ce idan ta sadu da mijinta sai ta ji jini ya tsinke mata. In kuma ba su sadu ba, komai tsawon lokaci babu tsikewar jinin nan. Shi ne take son don Allah don Annabi Malam ya taimaka mata da addu'a. Allah ya taimake mu gaba daya.
DAKTA YUSUF ALI: Malamai sun yi bayani a kan wannan. Annabi ya yi bayanin cewa irin wannan jini Shaidani ne. Wani Aljani ne a cikin Mahaifa yake bugun wata jijiya, sai wannan jinin ya rika zubowa, to amma wannan musamman shi ne ake cewa sihirin nazif, wato sammu ne na irin wannan na hana saduwa tsakanin mata da miji. To saboda haka yadda ake gane cewa wannan abu sammu ne, in ya zama sai lokaci daya ko sai a hali daya. A nan ne ake gane wannan abu sammu ne. Wato in ya zama sai wuri daya. Wannan gida ko wannan ofishi ko wannan kasuwar. Duk lokacin da mutum ya zo nan zai ji ransa ya baci ko ya ji kansa ya rika ciwo. Amma daga ya fita shi kenan, ko kuma duk sanda ya komoi gida ko ta komo sai ta rinka jin bacin rai, ba ta son ganin gidan. Amma in ta je wani gidan ko da za ta kewaye duniya za ta ji ba ta jin wannan bacin ran, ko kuma shi ma haka nan ne abin a gare shi mutumin. Duniyar nan in da za ta kallace su ba za ta ji ransa ya baci ba. Ko kuma a lokacin da mijin yake nan za ta ji ba ta son ganin sa ba ta kaunar ma ganin sa. Amma da zaran ya fita sai ta ji tana matukar kaunar sa. Haka nan shi ma kazalika. Amma daga ya bar gidan sai ya rika yabon ta a wurin abokansa. Wannan wuri daya kenan, kuma har yanzu mutum daya kawai kuma yanayi daya. Ya zama cewa mutum yana da mata misali dayar ba haka bane, abin da ya shafi rayuwar aure kullum za su yi, amma wannan kullum abu ya ki. Ko da ya zo ya kusance ta sai jini ya zo, ko kuma shi irin mai tafiya ne yana da wata sana'a a wani wuri a lokacin da ba ya gari ba jini, amma da zaran ya dawo gida ya ce assalamu alaikum sai jini ya zo, ba zai dauke ba sai ya ce "shi kenan sai na dawo," to wannan sammu ne. Saboda haka sammun nan kamar yadda ake kiran sa na maza Azzabadu ko al'akad, har yanzu yana faruwa a wurin mata. Wato kwatankwacinsa iri kamar guda biyar ne. Wannan daya ne daga ciki. Kuma duk hanyar warkar da su iri daya ce. Babu wani abu da ake karawa a kai. Duk daya ce da abin da zai zo ya karya sammu. Aljanu ne ake turo su, ake ba su wannan umurni, da ma da kun ga ya zo, to sai a kunna musu (green light), ana kunnawa shi ne, sai su zo su tsinke wannan jijiyar sai jini ya yi ta zuba. Yana tafiya, shi kenan, aikinsu ya gama. In da zai zauna wata guda bai zo ba, shi kenan ba za su yi wannan aikin ba. Yana zuwa shi kenan sai su zo.
Hanya mafificiya da Malamai suka yi bayani da ake bi a karya sammu shi ne a samu ganyen magarya koraye guda bakwai a dandaka su da dutse-dutse. A samu ruwa bokiti guda a zuba a kanta Ayatulkursiyyu da "Wa auhaina ila Musa. Kala Musa maji'itum bihi sihir. Inna ma sana'u kaidu sahir." "Makadabna" da kulliya da kulhuwallahu da falaki da nasi, sune guda tara kowacce kafa bakwai-bakwai a tofa. Hannun mai tofawar yana cikin wannan ruwa yana juya wannan ganyen, bakinsa yana kus da ruwan yana tofawa. Wato iskar bakinsa yana shafar ruwan. To idan an gama sai a diba hannu bibbiyu a sha sau uku. Sannan wannan ruwan a ba shi kullum da safe a diba a yi wanka da shi. Insha Allah wannan sammu zai karye.
Hanya ta biyu kuma akwai wanda ake samun kwai guda bakwai alal misali. Na farko ga abin da ake rubutawa, na biyu haka. Shi kenan har a gama. Idan aka gama sai a cinye. Wannan ma mujarrabi ne da ake karya sammu. Amma duk in tana neman maganin tsai da jini wannan duk ba zai yi ba. Ko'ina aka je komin wankin ciki sam-sam bai yi ba wannan shi ne.
TAMBAYA: Daga Hajiya Amina. Ina so Malam ya taimaka min da wata addu'a, yaro ne yake damu na da kuka cikin dare dan karami na goye. Sannan kuma da yayansa shi ma. Tambaya ta biyu shin wai gaskiya ne da ake cewa idan ba a sa wa yaro azurfa ba a wuya wai kansa ba ya tsayawa da wuri?
DAKTA YUSUF ALI: Wannan cuta gila ko gaila, wato a zamanin Manzon Allah (SAW) shi da kansa ya hana maza saduwa da matansu in suna da ciki. Ya ce wannan yana haddasa wannan cuta gila, ya sa yaro ya rame. Amma daga baya sai Manzo (S) ya ce wannan al'ada ta Larabawa ce. Wanda wannan wasu abubuwan da dama ba wai addini ya hana bane, ba wai wahayi ne ya sauka ba. A'a al'ada ce ta mutane, sai aka mayar da ita addini. Wannan shi ne ra'ayin Larabawa. Daga baya Manzo ya ga Yahudawa suna saduwa da matansu suna da ciki, amma wannan cuta ba ta faruwa a gare su, saboda haka sai ya warware wancan maganar ya ce ku ci gaba da saduwa da iyalanku suna da ciki. Kuma ai Malamai suna cewa saduwa da mace mai ciki yana kara wa dan gani da kuzarin jiki. Ka ga kenan maimakon a ce akwai cutarwa har ma amfani ake samu.
Maganar sa azurfa, to wannan gaskiya cikin abubuwan da aka kawo na tsari ni ban taba ganin maganar azurfa tana da wani tasiri a game da wannan abin da aka fada ba. Saboda haka wannan camfi ne kawai. Ba wani abu bane da za a kira shi addini ba.
TAMBAYA: Daga Mustafa: Malam idan mutum lokacin zakkarsa ya yi, sai yana da wasu kadarori kamar gine-gine ko kuma filaye, shin mutum zai kimanta da su ne don fitar musu da zakka?
DAKTA YUSUF ALI: In ya kasance gine-ginen da filayen nan ya saye su da nufin cewa siyarwa zai yi ya sake saye ya siyar, to su ma ai kayan sayarwa ne. Idan mutum ya zo zai fitar da zakka in ya lissafa kudin da ke hannu sai ya lissafa da su. To abin da ya kamata sai a fitar da zakka daga cikin wannan kudin. Amma idan gidaje ne kawai wadanda ba don siyarwa bane, wanda 'yan haya aka zuba a ciki, wannan kudin hayar ne za a fid da wa zakka, ba wai su kansu gidajen ba.
TAMBAYA: Malam ya yi mana fadakarwa a kan wasu 'yan shi'a da suka rika zagayawa gari ranar mauludi suna raba goro da cingam da alawa da turare da kudi na jan hankalin mutane, har ma wani tsoho ya samu N125 ya rika cewa ai su in za su rika samun irin wannan kowaye ma za su bi shi. Mai tambaya Sharif Sani Sharif daga Sharifai Kano.
DAKTA YUSUF ALI: Ni abin da zan ce mutane su yi aiki da hankalinsu. Su saurari masu wa'azi, su saurari manufofin 'yan shi'a, su saurari manufofin 'yan sunna, sannan su saurari manufofin wadansu ma, sannan su yi aiki da hankalinsu su ga wace hanya ya kamata su bi tunda Allah (T) cewa ya yi "La'ikraha fiddini." Ba dole a addini, wanda ya ga dama zai musulunta ya musulunta. Wanda ba zai musulunta ba shi kenan. Kuma a cikin suratul Kahfi Allah yana cewa Wanda ya ga dama ya musulunta wanda ya ga dama ya kafirta. Shi addini idan mutum zai yi don Allah, to ya yi don Allah. In kuma don kudi zai yi, to shi kenan ya je ya yi don kudi.
TAMBAYA: Allah ya gafarta Malam a zamanin mulkin Abbasiyawa an ce masu mulki daban, malamai kuma daban, amma sai ga shi kuma malamai kun kunno kai kun ce ku ma kuna so ku yi mulki, za ku tsaya takarar Shugaban kasa, Kananan Hukumomi da Gwamnoni, idan ku Malamai kuka kama mulki, yayin da kuka sha giyan mulki wa kuma zai fadakar da ku?
DAKTA YUSUF ALI: Wannan ina ji ai shi ne ra'ayina. Ni shi ne fahimtata. Amma yadda ka shigo da shi a wannan siga din Allah bai sa na fada ba, sai ka riga ni. Ai ba sai ka tafi daular Abbasiya ba. Ai ko yanzu ma ba ga kasashen da suke aiwatar da Musulunci ba. Ai ga Sudan nan. Ko ba ga irin su Saudiyya ba, ba ga irinsu Iran ba. Ai ka ga Malamai daban, Shehun nan Malamai daban. Kai kar ma in kai da nisa, ka dawo kasar nan ka dubi Shehu Dan Fodiyo, ai ka ga da ya gama jihadi kaf ya kafa daula, ai ka ga tashi ya yi ya koma wuri daya ya ci gaba da karantarwa. Ya ce kai Muhammad Bello kai ne Sarkin Musulmi a wannan bangaren, kai kuma Abdullahi Dan Fodiyo kai kuma kai ne a wannan bangare. Aka raba kasa gida biyu, wanan gabas, wannan yamma. Haka nan Shehu ya ci gaba da rayuwarsa yana koyarwa. Saboda ya nuna wa mutane Malami daban, kuma mai mulki daban. Saboda haka idan Abdullahi da Muhammad Bello suka samu matsala sai ka ga sun dawo gun Shehu Dan Fodiyo, shi zai warware matsalar. Saboda haka idan aka ce Malamai sune Gwamnoni an shiga uku. Kowanne ya samu aya bangaren kishiyansa ya shiga uku, zai sha yanka, zai sha konewa, zai sha kora da jafa'i. Saboda haka in ya kasance awaki ne suke rigima ko tumaki ka ga wannan su zaki duk za su iya zuwa su raba, amma in ya kasance su zaki ne suke rigima da shi da giwa, to wa zai zo ya raba? Ni ina ganin malamai su tsaya a matsayinsu na magada Annabawa. Wa zai mana addu'ar samun zaman lafiya? Wa zai mana fada in sabani ya faru a tsakaninmu. Amma daga zaran malamai sun shiga siyasa, duk abin da suka fada ba mai karba, kuma ba mai yarda. Za a ce kawai suna yi ne don siyasa ba don Allah bane. Amma idan Malami yana so ya yi siyasa, sai ya sauka daga kujerar malanta ya shiga makarantar siyasa.
Wassalamu alaikum.
Komawa babban shafinmu  Komawa saman wannan shafin