Tambaya ta 2
TAMBAYA: Ana cewa lokacin sujada ba a son karanta ayar Kur'ani, amma kamar yadda na taba tambaya a kwanaki can akwai wasu nafilfili da aka ce a raka'ar karshe za a karanta fatiha da Ayatul Kursiyyu da sauransu a sujadar karshe, to yaya za a yi kenan tunda ga maganar da ke cewa ba za a karanta sura a cikin sujada ba?
DAKTA YUSUF ALI: To yadda za a kawar da wannan shi ne akwai salla ta biyan bukata da aka ce mai raka'a 12, ina jin ita kake nufi, wacce za a yi ko dare ko rana raka'a 12, wacce ba za a yi sallama ba sai a ta karshe. Sai dai a yi tahiya a raka'a ta biyu a tashi kawai. In an kai 12 ba za a yi sallama ba sai a sake dungura goshi sannan a karanta fatiha din da Ayatul kursiyyu, wani da Kulhuwallahu da La'ilaha illahu wahadahu lasharika lahu. Sannan bayan wannan a karanta Allahumma inni as'aluka bi ma'akidil izzi min arshika wa muntaha rahmatika min kitabika wajadikkal a'ala wa kalimatikat tammati allati layujawizuhunna barrun wala fajirun an tusallimu wa tusalli ala Muhammadin wa ali-Muhammadin… sannan sai ka fadi bukatarka. Bayan ka gama wannan sai ka zauna ka ce assalamu alaikum, dama da hagu.
To in ka duba wadannan ayoyi Fatiha da Kulhuwallahu da Ayatul kursiyyu ba a ainihin cikin sallar aka karanta ba, a wani abu ne daban wanda shi ba sallar bane. Ai salla ka riga ka gama ta. Daga baya ne ka tsuro wata sujada kawai ka yi. Da a ce lokacin da kake sallar, a raka ta farko har zuwa 12, sannan ne ka yi wannan karatun, to a sannan ne za a ce kila ko ka ci karo da wancan hadisi, wanda Manzon Allah ya hana Sayyidina Ali karatun Kur'ani a cikin ruku'u ko sujada.
To amma wannan ba a cikin salla bane. Irin su da dama. Akwai sallar biyan bukata da za ka ga ana yin salatin Annabi, a yi subahannallah walhamdulillah wala'ilaha illallah, walahaula wala kuwwata illa billahil azim, kuma a zo a karanta ayar Kur'ani Rabbana ataina fiddunya hasanatan wal fil akhirati hasanatan wa kina azaban nar. Amma ita wannan sai an yi sallamar sannan a sake komawa a dungure.
Kodayake shi ma kansa yin karatun Kur'ani a cikin sujada din akwai sabanin Malamai. Wadansu sun ce a ma karanta din. To ka ga tunda an samu wani Malamin ya ce a ma karanta, ka ga shi kenan, kana iya makalewa a wannan ra'ayin nasa shi kenan ba tare da ka yi kowane laifi ba kenan.
Komawa babban shafinmu  Komawa saman wannan shafin
|