Ilimi Kogi Ne: |
Mai karatu wannan shi ne filin Ilimi Kogi da Ustaz Yusuf Ali ya yi ranar Laraba 4 ga Satumba, 2002. |
Tambaya ta 4
TAMBAYA: Muntari Sharifai ne. Akramakallah kamar a Makka wajen jifan Iblis, da a kasa ake yi, to kuma a yanzu sai na ga an yi gada a saman nan da ake yin jifa da kuma wajen dawafi na Makka da ake yi kan bene, na ga lokacin Annabi babu shi da sahabbai, to shi ba za a ce masa bidi'a ba sai maulidi za a ce wa bidi'a?
DAKTA YUSUF ALI: To wannan ka ga kai ma ka ba da amsa. Shi ya sa na ce ba wai abin da Manzo bai yi ba shi ne za a ce ba za a yi ba a Musulunci, a'a wanda ya hana kawai. Ka ga ga wurin jifan nan yadda aka canza shi, ka ga a zamanin Manzon Allah, ba ma shi ba a zamaninmu, da ai Mina shema ce kawai ta gwado, amma yanzu dubi yadda aka dabe wurin da dabe irin wanda za ka shigo gidan rediyon nan, duk haka aka bi shema aka dabe ta, alhali wannan gun da fa tsakuwa ce da kasa da burji, amma yanzu sai ka ga ko a kan titin da ke tsakanin shema da shema ma za ka iya zama ka kwanta. Sannan kuma sheman nan ga iyakondishin, bayan Annabi (S) da ma mu kanmu cikin rana ne da iska, haka nan fa muke, amma yanzu ga shi tanti aka kawo mai tsada wanda wuta ba ta kama shi aka zo aka saka lantarki, ko'ina haske ne ba ya mutuwa, kuma ruwan sha ga shi nan na kankara ne. Yanzu fa a cikin irin wannan ake zama a yi aikin hajji. Motoci da yanzu ake shiga, shi Annabi a kan rakuma ne da jaki. Wannan duk bidi'a ce.
Wannan ma da sauki, in ka dubi ita sallar fa ta tarawi, kuma da can kafin yanzu, da ai Limamai har guda hudu ne, Limamin Malikiyya daban, Limamin Shafi'iyya daban, Limamin hambaliyya daban, Limamain Hanafiyya daban, amma yanzu sai aka hade su aka yi Limami daya.
Sannan in ka dubi rijiyar zamzam, ko kuma hajrul Aswad din nan da mukamu Ibrahim duk da a jiki yake, sai aka ciro shi aka aje shi waje daya, wanda a zamanin Annabi ba haka aka yi ba.
Sannan kuma za ka ga ana yin tahajjudi. Shi tahajjudin nan waye a cikin wadanda suka isa a yi koyi da su ya yi yadda ake yi din nan? A ce za a zo a taru a masallaci, ba fa sallar tarawi ba, ita ma fa tarawin bida'a ce, to amma duk da haka a zo a tahajjudin nan, lokacin da ake yi ka ga yara sun zo da tabarmi da abinci, an yi wannan a zamanin Manzon Allah?
Ko kuma a ce a sauke Alkur'ani a sallar asham har a zo a yi khatama, Annabi ya yi? Sahabbai sun yi? Wani wanda ya isa a yi koyi da shi ya yi?
Ko kuma a zo a yi kunuti din nan. Kowace rana a karshen wannan sai an zo an yi wata doguwar kunuti, wanda za a yi addu'a. A yi wa mutanen gari, a yi wa sarakuna, a yi wa kasashe, a yi wa mata, a yi wa yara, a yi wa matasa; a dade ana yi. Annabi duk bai yi wannan ba. Kuma bai ce a yi ba.
Amma mu duk irin wannan, mu ba mu ce a'a ba, tunda mu ba sandararru bane. Addinin Musulunci addini ne wanda ya kasance mai fadi, na ci gaba, wanda zai iya da kowane irin canje-canje ya samu. Ba sandararre bane.
Ko kuma a'a idan ana jiran Liman ya fito sallar idi a hau kan mumbari a yi ta zikiri. Kullum fa sai sun hau kan mumbari, har Liman ya zo, har a yi kiran salla, zikiri ake yi fa, a yi ta zikiri, amma a yanzu sai ka ji wai masu yin zikirin kuma a ce kafirai, alhali kuma ga shi a masallacin Madina, a masallacin harami, kullum za ka ji suna yin zikirin nan - subhanallahi, walhamudlillahi, wallahu akbar, wa la'ilaha illallah, wa sallallahu ala Sayyidina Muhammad wa ala alihi wa sahabihi, allahu akbar. Haka fa za a yi ta yi, za a yi ta yi.
Saboda haka sai ka ga cewa in su suke yin abinsu sunna ne, in wani yake yi bidi'a ce. To wannan ba insafi bane gaskiya. Kuma sannan in ma za a ce abin nan da kake yi bidi'a ne, ko abin da kake yin nan bidi'a ce, to waye ya ce bidi'a gabaki dayanta haramun ce? Tunda Annabi (S) ya yi kira ma da a yi bidi'an nan. Ya ce "Man sanna sanatana hasanatan falahu ajaruha wa ajaru man amila biha ila yaumul kiyama." Watau wanda ya sunnanta wata sunna, wacce da ba ita, shi ne ya kirkiro ya sunnanta ta, ladan da ya kirkiro ya tabbata gare shi da ladan wanda ya yi aiki da ita har zuwa ranar lahira. Haka kuma Annabi (S) ya ce wanda ya sunnata sunna mummuna, to laifin na kagowar na nan a kansa, haka kuma wanda ya yi aiki da ita aka ba shi zunubi sai an ba ka irinsa.
Ma'ana kenan sunna kyakkyawa ake so a kawo. "Man ahadatha fi amrina haza ma laisa minhu fahuwa raddun," da ake yawan kawowa, wanda ya kirkiro wani abu, ya farar da wani abu, wanda ba ya cikin al'amarinmu. Annabi ya ce wanda ba ya ciki. To idan kuma yana ciki fa? To kuma "Alyauma akamaltu lakum dinakum..," a yau muka cika addini ya wanzu shi kenan, duk abin da ka zo da shi tunda an saukar da ayar karshe ya zama kari. A'a ai Annabi (S) sad da aka saukar da "Alyauma akamaltu lakum dinakum," ba shi kenan kawai kuma sai ya bace aka daina ganin sa ba. Wasu na cewa ya yi kwana 40 gaba, wasu ma sun ce ya fi haka kafin ya rasu. Kenan ka ga ya yi hukunce-hukunce, an saukar masa da wasu ayoyi. Shi ya sa ma malamai suke cewa ai ba wannan ce ayar karshe ba. "Wattaku yauman turja'una fihi ilallahi summa tuwaffa kullu nafsin makasabat layuzlamuna ," (bakara) ita ce ayar karshe. Saboda Sayyidina Umar yana cewa ita ce ayar karshe. Saboda Manzon Allah (S) shaida a kan haka har ya yi wafati bai fassara musu ita ba. Ayatur riba sune ayoyin karshe.
Saboda haka wannan mulahadha da ka kawo tana da muhimmanci kwarai da gaske. Ya kamata mutane su tabbatar da cewa kar su dauka tahajjudi da ake yi din nan wata sunna ce don ganin wadansu mutane ne suke yi. Ba mu ce kar a yi ba. Kamata ya yi kowa ma idan yana da dama ya yi. Amma ka ce wannan sunna ce, wani kuma wanda yake yin wani abu wanda shi ma ya ga dacewarsa ( ba daidai ba shi ne abin da muke ki). Akwai hadisin Ibn Mas'ud "Mara'ahul muslimuna hasana, fahuwa indallahi hasana." Abin da musulmi suka ga cewa kyakkyawa ne, to a gurin Allah ma kyakkyawa ne. A ce wasu mutane sun ga wani abu kyakkyawa suna yi suna da wata hujja da suka dosano ko daga Kur'ani ko daga hadisi ko daga maganar wani malami, su wannan nasu su ba daidai bane, naka wanda ka kirkiro din nan, wanda ba ka da hujja shi ne sunna, bayan kuma cewa Annabi (S) ko a halin tafiya ko a zaman gida bai taba karawa bisa ga raka'a 11 ba. To amma raka'a nawa ake yi a yanzu a haramin Makka, raka'a nawa ake yi a Madina?
Komawa babban shafinmu  Komawa saman wannan shafin
|
|