Ilimi Kogi Ne Filin Shirin asmsa tambayoyin masu sauraron daga Ustaz Yusuf Ali

Filin amsa tambayoyin masu saurare daga Ustaz Yusuf Ali
Juma'a 27 Rajab, 1423                



 Maigida da Uwargida | TAMABAYA TA 1  | TAMBAYA TA 2 | TAMBAYA TA 3 | TAMBAYA TA 4 | TAMBAYA TA 5 | TAMBAYA TA 6 | TAMBAYA TA 7 
Ilimi Kogi Ne | TAMBAYA TA 8
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
Ilimi Kogi Ne:

Mai karatu wannan shi ne filin Ilimi Kogi da Ustaz Yusuf Ali ya yi ranar Laraba 4 ga Satumba, 2002.

Tambaya ta 3

TAMBAYA: Daga Mahmud ne. Akramakallah ba ni da wani buri illa in zama Hafizul Kur'ani. Na yi kokari, ta nafilfili ne da addu'o'i da sauransu, amma ban samu wani abu da zai taimaka min hadda ta zauna min ba. Abu na biyu yarinya na haifa na sa mata sunan Mahaifiyata, a yanzu ta yi kusan shekara daya da 'yan watanni. Yayin da aka haife ta kamar ba ta da kashi, ana nan ana ta addu'o'i abin ya soma sauki, amma a yanzu haka zama ma ba ta iya yi. Shi ne nake so a taimaka min da wata addu'a da zan rika yi kan wadanan al'amura guda biyu.

DAKTA YUSUF ALI: Wannan yarinya Allah ya ba ta lafiya. Shi haddace Alkur'ani babu shakka cewa akwai addu'o'i da ake yi. Ko da ma a zaman tsangaya ne Alkur'ani din nan ba haddatuwa yake ta dadi ba, ana hadawa da su fafau da kafin tilawa, wasu ma har sukan sha jinnu, asiri na aljanu don dai su samu haddar Kur'ani. To yanzu alhamdulillahi irin wannan abu ya ragu, saboda yanzu an samu hanyoyi na haddace Alkur'ani masu sauki.

Na farko dai idan mutum yana so ya haddace Alkur'ani, lalle sai ya yi karatun tukuna. Idan ya kasance kana yi, ka tabbatar da cewa lallai fa sai kana bin musamman sabuwar tilawa. Idan kana bin ta sabuwa-sabuwa, to babu shakka za ta zo ta zauna maka. Don kodayaushe haddace aya daya ma ya fi karanta aya dubu. Wasu malaman ma sun ce ya fi kayan rakumi na ilimi wanda shi ba haddacewa aka yi ba. An ce duk wanda yake karanta Alkur'ani da aya biyar-biyar, to babu yadda za a yi ya manta shi.

Na biyu kuma akwai abubuwan da suke taimakawa wajen haddar Alkur'ani. Idan ya kasance a allo kake rubutawa, to kada ka canza wannan allon, don in kana tilawar za ka rika hango shi. To amma in kana yawan caccanzawa sai ka ga abin ya rikice maka. In kuma kana yi da Kur'ani ne, to ya kasance kana yi da Kur'ani guda daya, wanda kodayaushe ka san shafinsa. Ka san yanzu kana shafi kaza ka koma shafi kaza. To amma in kana caccanza wadanda shafukansu suka sha bamban, to shi ma wannan yana kawo rikicewar tilawa.

Abin da ake bukata shi ne abin da ka karanta yau ka haddace, to za ka maimaita shi sau biyar misali da ka. Wanda ka karanta jiya, ka maimaita shi sau hudu. Na shekaranjiya ka maimaita shi sau uku. Na shekaranjiya waccan ka maimaita shi sau biyu. Sannan kuma na shekaranjiya waccan waccan ka maimaita shi su daya. To in ka tafi a haka, ka tafi a haka, to har abada tilawarka ba za ta zube ba ta wannan ka'ida.

To amma duk da haka ana son wani abu da zai sa kuma tilawar ta zauna. To a irin wadannan abubuwa shi ne kamar yadda Imamu Suyudi yake cewa a cikin littafinsa da ya yi saboda ilimin Kur'ani, karanta ayoyi goma kafin mutum ya yi barci, to wannan zai sa duk abin da ya karanta na Kur'ani ba zai manta ba. Sune "Alif Lam Mim" zuwa "muflihuna," da "Ayatul Kursiyyu" zuwa "khaliduna." Sannan "lillahi mafis samawati wa ma fil ard" har zuwa karshen sura, wato ta Makara kenan. Wadannan ayoyi ne 12, kullum a ce bayan sallar isha in ka zo za ka kwanta ka karanta su, to insha Allahu tilawarka ba za ta zube ba.

Haka nan karanta "Inna fi khalkis samawati wakhtilafil ardi wannahari walfulkillati tajri fil bahari bima yanfa'un nasa wama anzalna minas sama'i min ma'in…likaumin ya'akilun", ita ma in kana karantawa tilawarka ba za ta zube ba. To irin wadannan ga su nan, fa'ida ce an ba ka.

Sai kuma maganar ita wannan yarinya, akwai abubuwan da mu muka jarraba a kan irin wannan. Akwai ayoyi na rukiyya guda shida na cikin Alkur'ani da ayatus shifa da kuma wadansu addu'o'i irin su "A'uzu bi kalimatillahi tammati min sharri ma khalak. Bismillahi lazi layadhurru ma'a ismihi shai'in ma fis samawati wa ma fil ardi wahuwa sami'ul alim." Da kuma "A'uzu bi kalimatillahi tamma min kulli shaidanin wahamma wa min kulli lamma." Sannan kuma irin su "Bismillahi alkika min kulli da'in yunzika wa min kulli sharri aini hasidin Allahumma rabban nas azhabil bahsi antas shafi la shifa illa anta …" Sannan kuma a koma kan rukiyya irin ta mayu: "Allahumma zas suldanul azimi wa mannil kadimi wa hiya kalimatit tamma wa du'a'il mustajaba hafi (sai ka fadi sunanta a nan) min anfusihim wa a'ayunin nasa illa habasun habisun washihabin kabisun…farji'il basara haltara min fudur, summa irji'il basara karrataini yankalibu ilaikal basaru khasi'an wahuwa hasir." Sannan sai ayatus shifa, ina jin kuma na fade su.

Wadannan yadda ka ji na fade su haka nan zai kasance a tofa su a ruwa, yarinya ana mata wanka safe da yamma tana sha, kwana uku a sake tofawa. Da haka har a samu sati hudu. Kuma a tofa shi a cikin man zaitun, ya kasance ana ba ta da karamin cokali safe da yamma, kuma ana shafe wannan jikin nata da shi. Sannan a rika karanta mata wadanan abubuwa ko kuma da kaset kullum a kunnenta safe da yamma. Insha Allahu in ba ta zama, ko kanta ba ya zama, ko ba ta iya yin magana, halinta ya zo ya daidaita. Insha Allahu wata ran, in dai an yi wannan za ka bugo waya ka ce ga yadda halin wannan yarinya ya kasance. (Mafi dacewa a nemi rubutattun ayoyin daga Shehi, don a tabbatar an karanta su daidai).

BAYANIN USTAZ: Ka ga an kare mutane daga zuwa wajen macuta, bokaye da sauransu, an mai da su ga koyarwar Allah. Kuma ina yin wannan ne ba don komai ba sai don saboda aiki da abin da Allah (T) yake fada "Innallazina yaktumuna ma anzalna minal bayyinati walhuda min ba'adi ma bayyannahu lil nasi fil kitabi ula'ika yal'anuhumullah wa yal'anuhumul la'inun." Wato hakika wadanda suke boye abin da muka saukar a cikin littafi na daga bayani ga mutane, to wadannan Allah yana tsine musu, kuma masu tsinewa (Mala'iku ne, aljanu ne da mutane) su ma suna tsine musu.

Kuma har yanzu Annabi (S) ya ce, wanda ya san ilimi ya boye za a yi masa a ranar lahira linzami da linzamin wuta. Shi ya sa ka ga sahabbai da yawa Annabi (S) zai kebance su da wani ilimi ko da wata hikima ko wani abu, amma su ki gaya wa kowa har sai sun tabbatar cutar ajali ce ta zo musu, sai su tara mutane su ce, to ga abin da Annabi ya sanar da mu wata ran, zan bayyana muku saboda tsoro hadisin can. Saboda haka su irin wadancan mutane ba su nake jin tsoro ba Allah Mahaliccina nake ji. Ba kuma ina aiki da maganarsu bane, ina aiki ne da maganar da Allah da Manzonsa suka fada.

TAMBAYA: Awwalu ne daga Goron Dutse. Ina yin godiya ga Malam da kuma addu'a. Abin da ake yi din nan Allah ya saka wa Malam da alheri.

Komawa babban shafinmu                   Komawa saman wannan shafin