Ilimi Kogi Ne Filin Shirin asmsa tambayoyin masu sauraron daga Ustaz Yusuf Ali

Filin amsa tambayoyin masu saurare daga Ustaz Yusuf Ali
Juma'a 27 Rajab, 1423                



 Maigida da Uwargida | TAMABAYA TA 1  | TAMBAYA TA 2 | TAMBAYA TA 3 | TAMBAYA TA 4 | TAMBAYA TA 5 | TAMBAYA TA 6 | TAMBAYA TA 7 
Ilimi Kogi Ne | TAMBAYA TA 8
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
Ilimi Kogi Ne:

Mai karatu wannan shi ne filin Ilimi Kogi da Ustaz Yusuf Ali ya yi ranar Laraba 4 ga Satumba, 2002.

Tambaya ta 1

Tambaya. Malam Bashir ne. Ina wa Malam maraba da zuwa. Kuma Alhmadulillahi fushinmu ko kukanmu, Allah ya yaye. Bayan haka Malam na ji labarin an samu ci gaba, muna taya ka murna. Allah ya dada turawa gaba. Lokacin da Manzo ya yi isra'i akwai lokacin da aka ce masa Ubangijinsa yana sallah, shi ne ni ban gane menene ake nufi da wannan ba.

DAKTA YUSUF ALI: Lokacin da Annabi (S) ya yi mi'iraji da isra'i, daga cikin hadisai, musamman in aka duba littafin Mawahib Addiniyya, a takaicewarsa na shi Yusuf Annabhany ya kawo wannan magana cewa Annabi (S), lokacin da ya yi mi'iraji, sad da ya kasance babu Mala'ika Jibrilu, babu sauran kowa, ya zama daga shi sai Allah din, sai ya ji wata murya, ta ma Sayyidina Abubakar, don saboda ya samu natsuwa, an ce da shi ai sai ka dakata Ubangiji din yana sallah. To sai ya dakata.

Babu shakka shi ma Manzon Allah (S), wadannan abubuwa guda biyu sun tsaya masa a zuciya. Saboda haka, sad da ya zo ganawa da Allah (T) bai yi wata-wata ba sai ya ce "Akwai abubuwan mamaki da na ji. Na farko dai na ji an ce kana sallah, kuma na ji murya kamar muryar abokina Abubakar, yaya aka yi wannan lamari?" Sai aka ce "Mun halicci Mala'ika ne mai murya irin tasa don ka samu natsuwa. Cewar kuma ina sallah ba ka ji bane ina cewa, "huwallazi yusalli alaikum wa mala'ikatuhu liyukhrijakum minaz zulumati ilan nur, wakana bil muminina rahima." Wannan shi ne, salati nake yi a gare ku, kuma salatina rahama ce." Kuma akwai wata ayar tana cewa "Innallaha wamala'ikatuhu yusalluna alal nabiyyi, ya ayyuhallazina amanu sallu alaihi wa sallimu taslima." Allah (T) da kansa yana yin salati, mala'ikunsa suna yin salati ga Annabi (S), saboda haka mu ma aka ce mu yi.

Wannan madda ta salla, yusalli, salatan, salla ya yi salla, yusalli - yana sallah, salatan sallah, ita ce za ka yi amfani da ita ba tare da ka canza komai ba salla ya yi salati, yusalli yana salati, salatan salati. Saboda haka babu wani bambanci. Saboda haka tana iya daukar ma'anar salati Allah (T) yake yi, saboda kalmar yana sallah daidai take da yana salati. Wannan shi ne abin da su Malamai suka yi bayani a kai. Allahu a'alam.

Komawa babban shafinmu                   Komawa saman wannan shafin