Ilimi Kogi Ne Filin Shirin asmsa tambayoyin masu sauraron daga Ustaz Yusuf Ali

Filin amsa tambayoyin masu saurare daga Ustaz Yusuf Ali
Juma'a 27 Rajab, 1423                



 Maigida da Uwargida | TAMABAYA TA 1  | TAMBAYA TA 2 | TAMBAYA TA 3 | TAMBAYA TA 4 | TAMBAYA TA 5 | TAMBAYA TA 6 | TAMBAYA TA 7 
Ilimi Kogi Ne | TAMBAYA TA 8
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
Ilimi Kogi Ne:

Mai karatu wannan shi ne filin Ilimi Kogi da Ustaz Yusuf Ali ya yi ranar Laraba 4 ga Satumba, 2002.

Tambaya ta 5

TAMBAYA: Malam Abubakar ne. Akramakallahu nine na sami sallar isha raka'a daya, to da na tashi sai na yi karatu a bayyane, to shi ne wani mutum ya ce min ba haka ake yi ba. Shi ne nake so Akramakallahu ya yi min karin bayani.

DAKTA YUSUF ALI: Abin da ya kamata ka yi shi ne raka'a daya ka samu, da ka tashi bayan sallama ka ga akwai sauran raka'a uku a gabanka, to sai ka yi raka'a daya a fili, ta biyu ma sai ka yi a fili, ta karshe sai ka yi ta a asirce. To ka san akwai maganar gini da sauransu. Kamar tsuntsu ne a sama yana tashi, sai ka ga nan ga fukafuki, nan ga fukafuki, nan ya zanke, nan ya zanke, to haka nan sallarka take kenan. Nan fukafuki, tsakiya da kai, can kuma fukafuki. Nan ka yi 'yar gajeriya ta Liman wanda Fatiha kawai ya karanta, saboda haka ana neman ka raka'a biyu dogaye a tsakiya masu Fatiha da Sura, kuma za ka kawo su kamar yadda Liman ya kawo su - karatu a bayyane. Sannan kuma ana bin ka raka'a daya marar sura, ita ma gajeriya irin ta Liman. Saboda haka nan gajeriya, can gajeriya, tsakiya doguwa. Shi ne "zatul janahaini," kenan.

Amma wannan bai sa ko da ba a bi ba, tunda a mazhabar Malikiyya ba'adi ta kama ka saboda ka yi kari a inda babu kari, wato wannan bayyanawar da ka yi, ka bayyana a inda ba a bayyanawa, wato raka'ar karshe da ka bayyana, ka ga wannan kari ce wacce ka karanta fatiha. Amma wasu malamai suna ganin ko da ba ka yi sujadar rafkanuwa ba shi kenan sallarka ta yi. A yanzu dai za mu ce ba wata gyara da za ka yi ta yi, tunda wani abu ne da ka yi shi a kuskure.

TAMBAYA: Muhammad Hafizu ne daga Karamar Hukumar Fagge. Akramakallah muna maka barka da zuwa. Ni zan dakatar da tambayata in bar wa jama'a filin sai dai wani makon in Allah ya kai mu.

Komawa babban shafinmu                   Komawa saman wannan shafin