Ilimi Kogi Ne Filin Shirin asmsa tambayoyin masu sauraron daga Ustaz Yusuf Ali

Filin amsa tambayoyin masu saurare daga Ustaz Yusuf Ali
Juma'a 27 Rajab, 1423                



 Maigida da Uwargida | TAMABAYA TA 1  | TAMBAYA TA 2 | TAMBAYA TA 3 | TAMBAYA TA 4 | TAMBAYA TA 5 | TAMBAYA TA 6 | TAMBAYA TA 7 
Ilimi Kogi Ne | TAMBAYA TA 8
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
Ilimi Kogi Ne:

Mai karatu wannan shi ne filin Ilimi Kogi da Ustaz Yusuf Ali ya yi ranar Laraba 4 ga Satumba, 2002.

Tambaya ta 6

TAMBAYA: Muhammad Sani ne daga Kano. Bayanin da ka yi a kan karin basira, musamman lokacin jarabawa mai ayar Kahafi ta goma, don Allah a taimaka Malam a yi mana bayanin yadda ake yi.

DAKTA YUSUF ALI: Yadda ake yi shi ne idan ya kasance an ce an sa ranar jarabawa, ko an kafe 'timetable' na jarabawa, to a sannan ne za a fara yin wannan addu'a. Wannan aya ta kahafi - "rabbana atina min ladunka rahamatan wahayyi'ilana min amrina rashada." Ita za a karanta 313. Kullum za ka yi 313, salatin Annabi 500, haka za ka yi ta yi har ranar jarabawa ta zo. In ranar jarabawa ta zo ba dainawa za ka yi ba. Idan kuma an ce ga shi za a shiga dakin jarabawa, nan ne za ka yi salatin Annabi 10. Idan an ba da takardar jarabawa kafin ka buda ka yi salatin Annabi goma, saboda salatin Annabi budi ne na fahimta, budi ne na samun ilimi, yana da fa'ida kwarai da gaske. Idan kuma ka buda kafin ka fara amsawa sai ka sake karantawa, ka ga ka samu wajen 30 kenan. Kuma salatin nan ba wai sai dogo ba. "Allahumma salli ala Sayyidina Muhammadin wa sallim" ma shi kenan. Sannan kuma duk sad da ka ga wata tambaya ka kasa amsawa, ko ka san ta ka manta, sai ka yi salatin Annabi goma, ka ce "Allahumma zakkirni ma nasitu." Allah ka tunatar da ni abin da na manta.

Malamai kuma suka ce idan kana so ka yi karatun ne yadda ba ka so ka manta ko da harafi, to duk sad da ka zo daukar darasi, wanda ko da ran jarabawa sai ya zo maka sai ka ce "Allahumma fatah alayya hikmataka wanshur alayya rahamataka, ya arhamar rahimin." Sai ka karanta sau daya ka dauki karatunka.

Komawa babban shafinmu                   Komawa saman wannan shafin