Ilimi Kogi Ne Filin Shirin asmsa tambayoyin masu sauraron daga Ustaz Yusuf Ali

Filin amsa tambayoyin masu saurare daga Ustaz Yusuf Ali
Juma'a 27 Rajab, 1423                



 Maigida da Uwargida | TAMABAYA TA 1  | TAMBAYA TA 2 | TAMBAYA TA 3 | TAMBAYA TA 4 | TAMBAYA TA 5 | TAMBAYA TA 6 | TAMBAYA TA 7 
Ilimi Kogi Ne | TAMBAYA TA 8
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
Ilimi Kogi Ne:

Mai karatu wannan shi ne filin Ilimi Kogi da Ustaz Yusuf Ali ya yi ranar Laraba 4 ga Satumba, 2002.

Tambaya ta 7

TAMBAYA: Naziru ne daga Bakin zuwo. Muna wa Malam barka da zuwa. Duk bayanin da Malam ya yi kan mauludi mun gamsu, muna kuma daya daga cikin masu yi. To amma kuma karin bayanin da muke so malam ya kara yi mana shi ne kan irin mauludin nan da 'yan makaranta suke yi. Gaskiya wani lokacin za ka ga 'yan makaranta sun zo mauludi 'yan mata sun ci kwalliya, sun hau mumbari suna rawa suna karatuttuka, samari sun zo sun gewaye su, sannan kuma mu nan suna kwana suna mauludi, gaskiya sukan dan shigar mana hakki a wajen buge-bugen mandiri. Shi ne muke so Malam ya yi bayani, shin wannan ya yi daidai ko kuwa akwai wani abu?

DAKTA YUSUF ALI: To ai ko da ma da aka ce mauludi ya halatta, to ai kuma ba a ce a yi wani aikin munkari ba. Su ma malaman da suka ce mauludin ya halatta irin su Imam Suyudi ai ba cewa suka yi a shigar da wasu ayyuka wadanda suke marasa kyau ba, addinin Musulunci bai yarda da su ba. Kamar cudanyar maza da mata, kamar kuma yin wadansu wakoki, kila ma ba na yabon Annabi ne ko na Musulunci ba, ko ya kasance da wasu abubuwa da za su jawo habaici ko fada ko wani abu. To irin wadannan sune ba a so. Ko kuma ya zama yin mauludin ya jawo saryarwar wata farillar, kamar ya zama mutane su kwana suna yin mauludin, amma wajen asuba su yi barci ba su sami damar sallar ma asuba ba. Ka ga wannan ba yadda za a yi a hada mauludi da sallar farilla. Saboda haka in mauludi ya zama haka, to babu shakka ba shi ne irin mauludin da ake cewa kyakkyawa ba, wannan ya zama mauludi ne mummuna. Kodayake kuma irin sa don saboda ba shi da yawa, bai kamata don ana yi can daya, nan ga guda goma ba irin wannan, ka ce duk gaba daya haramun ne, ko kuma duk gaba daya ba za a yi ba. Kokari za a yi irin wadannan mutane a jawo hankalinsu. Saboda haka a yanzu ma muna jawo hankalinsu a kan cewa lalle ya kasance an tsarkake mauludi, duk wani taro na addinin Musulunci a tsarkake shi, ba wai sai lalle taron mauludi ba. Ya kasance duk abin da aka ce a nisance shi, to a nisance shi. A nisanci cudanya, cudanyar nan tana da muni kwarai da gaske tsakanin maza da mata baligai. A nuna wa su 'yan mata yadda shigar Musulunci take da kuma yadda za su sarrafa kansu a sad da suke tare da wasu ajanabiyyai, abin da ya shafi muryarsu, abin da ya shafi surarsu. Ba daidai bane a ce mace ta zo baliga, kuma tana rawa a gaban maza ma musamman. Kila wasu suna yi amma ni ban gani ba, in akwai masu yin wannan, to a yi kokari cewa su daina.

Game kuma da cewa ana hana mutane barci da sauransu, wannan ma ya kamata mutane su rika lura da hakkin jama'a. Irin wadannan abubuwa din, musamman idan dare ya yi, ko dai ya zama in akwai irin wannan bukatar, in dare ya yi sosai a rika rusunawa. Ba wai mauludi ne kawai hanyar da za a nuna kauna ga Annabi (S) ba, balle a ce wanda ba ya yi ba mai kaunar sa bane, a'a kowa akwai hanyar da ya zaba. Shi Annabi hanyoyin da za a nuna ana kaunar sa suna da yawan gaske. Allah ya sa su masu irin wannan din sun ji.

Komawa babban shafinmu                   Komawa saman wannan shafin