Ilimi Kogi Ne: |
Mai karatu wannan shi ne filin Ilimi Kogi da Ustaz Yusuf Ali ya yi ranar Laraba 4 ga Satumba, 2002. |
Tambaya ta 8
TAMBAYA: Musa Nasidi ne. Tambayata ita ce a Madina na ga an sa wani allo daga inda Liman yake a tsaye, sai su ce kar ka haura daidai inda yake, dole ka koma bayansa. Idan wai ka yi salla gaban Liman, sallarka ba ta yi ba. Akaramakallah su a ina suka samo wannan?
DAKTA YUSUF ALI: Ka san ka'ida yadda take ta sha'anin Liman da Mamu wajen abin da ya shafi yin salla, abin da ake so lalle ya kasance shi mamu kodayaushe yana bayan Liman. Kar ya kasance a sama da shi, kar ya kasance a gabansa. Wannan ka'ida ce ta kowace mazhaba. To amma wannan ba ana nufin cewa kuma in ka yi salla gaban Liman sallarka ba ta yi ba, ko sallarka ta baci, sai dai a ce makaruhi. Ka aikata makaruhi, shi kuwa makaruhi wani abu ne wanda ya zama cewa aikata shi babu alhaki in ba ka yi ba ba wani lada, ko kuma in ka aikata shi ka samu lada, in kuma ba ka yi ba ba ka da zunubi. Ja'izi kuma shi ne wanda in ba ka yi ba ba lada, in ba ka yi ba babu alhaki. Amma duk malaman sun yi ittifaki a kan cewa ba za ka wuce gaban Liman din ba sai idan ya kasance babu fili ne a bayansa. Ba za ka hau gini saman Liman ba, sai idan ya zama babu fili a bayansa. Su ina ganin saboda kila sun ga ko akwai yalwar lokaci ne da yawa kar abin ya zama barababiya shi ya sa suka zo suka yi wannan. Za ka ga sun zo sun saka allunan da yawan gaske, an sassaka su. Dole idan ka zo sai ka tsaya. To amma ni a yadda na fahimta suna so su nuna maka kai daga waje ka gane ina ne sahun farko yake, saboda haka ka tsaya a sahun farko. In ka duba kuma gurin da fadin gaske,babu yadda za a yi ma mutum ya ce zai wuce gaba can a baya babu fili. Galibi sai ka ga mutane har cikin harami ga fili da shimfida da komai, amma sai ka ga sun zo waje sun cunkushe wajen, ina ga suna so ne a koma can ciki a rika abin nan.
Ko da mazhabarsu ce wadda suke cewa Hambaliyya ba ta nuna cewa don ka yi salla a gaban Liman sallarka ba ta yi ba, matukar dai akwai wani uzuri. Saboda haka yanzu in ka tafi masallatanmu na nan Kano, za ka ga yawanci tilas sai ka shiga gaban Liman. In ka tafi masallacin Murtala misali, za ka ga masallacin ma a baya can yake, ko kuma a tsakiya. To tilas ne mutane su wuce gaba can don kuwa bayan ba za a iya samun gurin da zai rike wadannan mutanen ba. Ba mu taba jin wanda ya ce hakan bai yi ba. Sannan kuma Malamai suka zo suka shata masallacin.
TAMABAYA: Mahmud ne ya dawo. Kaunarka ce ta cika min zuciya.
DAKTA YUSUF ALI: Allah din da ya sa ka so ni, to shi ma Allah ya so ka. Haka Annabi (S) ya ce a yi wanan addu'a sad da mutum ya ce yana son ka.
TAMBAYA: Tijjani Rabi'u ne dan uwan Khalifa. Muna wa Malam barka da zuwa. Sai dai in mun yi bege mu sa kaset kawai. Allah ya saka da alheri.
Komawa babban shafinmu  Komawa saman wannan shafin
|
|